19 Satumba 2025 - 16:19
Source: Quds
Falasdinawa 73 Ne Suka Yi Shahada A Gaza Tun Daga Safiyar Yau

Majiyoyin likitocin Falasdinu sun sanar da cewa adadin Falasdinawa 73 ne suka yi shahada a hare-haren da Isra'ila ta kai a yankuna daban-daban na zirin Gaza tun da safiyar yau, 11 daga cikinsu sun fito ne daga birnin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran Falasdinu sun bayar da rahoton shahadar akalla wasu 'yan kasar 73 su kai shahada sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a yankuna daban-daban na zirin Gaza da kuma harba makamai masu linzami a gidajen Falasdinawa a Ramallah.

Sojojin Isra'ila sun shahadantar da kalla Palasdinawa 73 a yankuna daban-daban na zirin Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila daga gabar tekun zirin Gaza sun kai hari kan birnin Khan Yunis da ke kudancin yankin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha